Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto KhadibZadeh yana fadar haka a jiya Litinin, a dai dai lokacinda firai ministan HKI Naftali Bennett ya isa birnin Abudabi na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ziyara irinta na farko wanda babban jami’an HKI ya kawo kasar.
Naftali Bennett ya gana da sarkin kasar UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a birnin Abudabi. Kuma ziyarar tana zuwa ne a dai dai lokacinda ake cika shekara guda da samar da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu a shekarar da ta gabata.
342/